Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya bukaci gudanar da wasu taruka tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya, da za a baiwa taken makon fahimtar juna da hadin kai tsakanin addinai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC an habarta cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya bukaci gudanar da wasu taruka tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya, da za a baiwa taken makon fahimtar juna da hadin kai tsakanin addinai na duniya baki daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa babban sakataren kungiyar ya bayyana hakan ne a cikin wani bayani da ofishinsa ya fitar, wanda kuma aka aike da shi zuwa ga cibiyoyi bunkasa harkokin al'adu da na addinai a kasashen duniya daban-daban, kiran da ake ganin ya samu karbuwa daga wasu gwamnatoci.
Kungiyar hada kan kasashen musulmi ta OIC dai na taka gagarumar rawa a bangarori da dama a duniya, musamman kan batutuwa da suka danganci kara kusanto da fahimta tsakanin musulmi da sauran addinai, ta yadda za a zauna lafiya tare da juna.
742662