IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Mai Tsarki Ta Duniya A Morocco

9:19 - February 07, 2011
Lambar Labari: 2076416
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a karo na shida a birnin Ribat fadar mulkin kasar Morocco, wadda aka za a bayar da kyautar sarki Muhammad na shida bayan kammala tag a wadanda suka nuna kwazo.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na marocjournal cewa, an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a karo na shida a birnin Ribat fadar mulkin kasar Morocco, wadda aka za a bayar da kyautar sarki Muhammad na shida bayan kammala ta ga wadanda suka nuna kwazo a dukkanin bangarorin da ake gudanar da gasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar karatun kur'ani ta samun halarat makaranta da mahardata daga kasashen musulmi da na larabawa 33, inda suke karawa da juna a bangarorin karatu da kuma harda, gami da ilmin sanin ka'idojin karatun kur'ani mai tsarki waito tajwidi.

Gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a karo na shida a birnin Ribat fadar mulkin kasar Morocco, wadda aka za a bayar da kyautar sarki Muhammad na shida bayan kammala tag a wadanda suka nuna kwazo, hakan zai karafa makaranta na kasar.

742630


captcha