Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da maulidin manzon Allah (SAW) a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda cibiyar bunkasa harkokin addinin muslunci ta birnin ta daukin nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wata mai kamawa.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na musulim centre an bayyana cewa, za a gudanar da maulidin manzon Allah (SAW) a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda cibiyar bunkasa harkokin addinin muslunci ta birnin ta daukin nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wata mai kamawa na rabi'ul awwal.
Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin musulmin kasar Birtaniya da suka hada mabiya tafarkin sunna da kuma mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah suna gudanar da taruka na bai daya domin raya ranakun maulidin annabi, da kuma gabatar da jawabai da makaloli kan rayuwarsa, da darussan da ke ciki ga musulmi.
Gudanar da maulidin manzon Allah (SAW) a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda cibiyar bunkasa harkokin addinin muslunci ta birnin ta daukin nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wata mai kamawa, na daga cikin ayyukan musulmin kasar Birtaniya.
742495