Bangaren kasa da kasa, Ana shirin fara gudanar da wani shirin bayar da horo ga yara 'yan makaranta na koyon karatun kur'ani mai tsarki tare da sanin ka'idojin karatu, da kuma sanin ma'anonin ayoyi, wanda za a gudanar a garin Kazimain.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muzn an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani shirin bayar da horo ga yara 'yan makaranta na koyon karatun kur'ani mai tsarki tare da sanin ka'idojin karatu, da kuma sanin ma'anonin ayoyi, wanda za a gudanar a garin Kazimain da ke arewacin birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.
Wannan shiri dai zai ebanci kanan yara ne masu shawar karatu kur'ani, kuma yanzu haka an riga an fara rijistar sunayen masu bukatar shiga cikin shirin a garin Kazimai da sauran yankunan da suke kusa da shi.
Wannan shirin bayar da horo ga yara 'yan makaranta na koyon karatun kur'ani mai tsarki tare da sanin ka'idojin karatu, da kuma sanin ma'anonin ayoyi, wanda za a gudanar a garin Kazimain yana da amfani ga yara masu zimmar koyon karatun kur'ani.
742489