IQNA

Za A Gudanar Da Tarukan Shekara-Shekra Na Musulmi A Kasar Faransa

11:54 - February 08, 2011
Lambar Labari: 2077461
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da tarukan shekara-shekara na musulmi a birnin Lille na kasar Faransa, wanda zai fara daga makon gobe har zuwa tsawon mako daya tare da halartar masana daga sassa na kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahabarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, za a gudanar da tarukan shekara-shekara na musulmi a birnin Lille na kasar Faransa, wanda zai fara daga makon gobe har zuwa tsawon mako daya tare da halartar masana daga sassa na kasar ta Faransa.

Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin gudanar da wannan zaman taro, malamai da kuma masana musulmi gami da wakilan cibiyoyin musulmin kasar Faransa za su gabatar da jawabai, da kuma gabatar da makalolin da suka rubuta dangane da muhimmancin fadada ayyuakn Musulunci.

A bangare guda kuma za a bude wani daki a gefen taron kide-kiden musulmi da kuma yadda suke isar da sakonsu ta wannan hanayar a cikin harshen faransanci, wanda hakan na daya daga cikin salon da suke bi na tallata addininsu.

743444
captcha