IQNA

An Buga Wani Sabon Babban Littafin Tarihin Musulunci A jami'ar Cambriedge

11:54 - February 08, 2011
1
Lambar Labari: 2077468
Bangaren kas ada kasa, An buga wani sabon babban littafin tarihin addinin muslunci a jami'ar Cambriedge da ke birnin London na kasar Birtaniya, domin amfanin masu nazari kan ilmomin tarihi a jami'ar da ma sauran jimi'oi na duniya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam Today an bayyana cewa, an buga wani sabon babban littafin tarihin addinin muslunci a jami'ar Cambriedge da ke birnin London na kasar Birtaniya, domin amfanin masu nazari kan ilmomin tarihi a jami'ar da ma sauran jimi'oi na duniya musamman na kasashen yammacin turai.

Littafin wanda masana tarihi suka hadu suka rubuta shi ya kunshi mujalladi shida, kowannensu yana shafuka akalla 800, haka nan kuma wannan littafi ya kawo bayanai dangane tarihin addinin Musulunci tun daga lokacin aiko ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a lokacin jahiliyar kuraishawa.

Bayan nan kuma ya kawo abubuwan da suka faru na tarhi da ayyada addinin muslunci ya samu karbuwa a yankin gabas ta tsakiya, da yadda ya yadu har zuwa wasu yankuna na gabacin nahiyar Asia, da kuma gabacin nahiyar turai gami da sauran yankuna na duniya baki daya.

Daga cikin abubuwan da ya mayar da hanakali kansu akwai rubuce-rubuce da aka yi kan tarihin irfanin muslunci, da kuma adabin yarukan larabci da farisanci gami da urdu, wadanda dukkaninsu yaruka ne da suka taka gagarumar rawa wajen yaduwar addini.

Buga sabon babban littafin tarihin addinin muslunci a jami'ar Cambriedge da ke birnin London na kasar Birtaniya, domin amfanin masu nazari kan ilmomin tarihi a jami'ar da ma sauran jimi'oi na duniya, zai taimaka ma masu nazarin addini baki daya.

743352


Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
usman abdullahi inusa
1
0
Inada buqatan tarihin Addinin musulunci ne saboda in Amfada dashi
captcha