Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Sharja nan kasar hadaddiyar daular larabawa, wadda ake yi wa lakabi da gasar Hasawi, da ke samun halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran wam na kasar hadaddiyar daular larabawa an bayyana cewa an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Sharja nan kasar hadaddiyar daular larabawa, wadda ake yi wa lakabi da gasar Hasawi, da ke samun halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar, da suka hada da dukkanin birane.
Bayanin ya ci gaba da cewa babban kwamitin shirya gasar karatu da hardar kur'ani na kasa shi ne ya dauki nauyin shirya wannan gasa, tare da hadin gwiwa da cibiyar da harkokin kur'ani da ke karakshin ma'aikatar kula da ayyukan addinin muslunci ta kasar.
Yanzu haka dai an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Sharja nan kasar hadaddiyar daular larabawa, wadda ake yi wa lakabi da gasar Hasawi, da ke samun halartar makaranta da mahardata na kasar baki daya.
743270