IQNA

Taron Hadin Guiwa Tsakanin Masana Ilimi Na Iran da na Ghana

Bangaren al'adu da fasaha;an gudanar da wani taron hadin guiwa da zummar yin masanyar ra'ayi kan fasahar musulmi inda masana harkokin fasaha daga kasashen Iran da Ghana a gidan tarihi na birnin Accra fadar mulkin kasar Ghana suka hallara.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an gudanar da wani taron hadin guiwa da zummar yin masanyar ra'ayi kan fasahar musulmi inda masana harkokin fasaha daga kasashen Iran da Ghana a gidan tarihi na birnin Accra fadar mulkin kasar Ghana suka hallara.Gudanar da irin wannan taron hadin guiwa ko shakka babu zai kara hada zumunta a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Ghama da kuma al'ummomin kasashen biyu da hakan kuma zai iya zaman darasi a ga sauran kasashen duniya.


743219