Bangaren kasa da kasa:hadin guiwar kungiyoyin musulmi a jami'ar Yurk na kasar Britaniya tana da shirin a ranar lahadi ashirin da biyar ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ya shirya wani taro na karawa juna sani da fadakar da al'ummar birnin na Yurk domin ta kara masu sani kan addinin Musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; hadin guiwar kungiyoyin musulmi a jami'ar Yurk na kasar Britaniya tana da shirin a ranar lahadi ashirin da biyar ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ya shirya wani taro na karawa juna sani da fadakar da al'ummar birnin na Yurk domin ta kara masu sani kan addinin Musulunci. Gudanar da irin wannan taro wani lamari ne mai matukar muhimmanci ta fuskoki da dama kuma daban-daban da kuma za su kara bunkasa lamarin zamantakewa da kara fahimtar jama'a dangane da addinin Musulunci.
743737