IQNA

Zangunan Bada Horo Kan Ilmomin Addininin Musulunci A Baljuim

Bangaren kasa da kasa;a ranar ashirin da biyar ga watan bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya za a fara gudanar da zangunan bada horo kan ilimomin da addinin Musulunci ta kumsa kuma a cibiyar al'adu ta Musulunci da ke kasar beljuim za a gudanar.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da biyar ga watan bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya za a fara gudanar da zangunan bada horo kan ilimomin da addinin Musulunci ta kumsa kuma a cibiyar al'adu ta Musulunci da ke kasar beljuim za a gudanar.Daga cikin fannoni da wannan zangunan ilimi zai kumsa ya shafi koyar da kur'ani,fikihu,Akhalaki,tarihin sirar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa. Kuma ajiyoyin wannan zangon karatu shi a ware kwanaki biyu a kowa ne mako lahadi da laraba.

743785