IQNA

An Bude Babban Masallacin Birnin Kolen Na Kasar Jamus

16:00 - February 09, 2011
Lambar Labari: 2078537
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da bukin bude wani babban masallaci a birnin Kolen na kasar Jamus, wanda jami’an gwamnati da suka hada magajin garin birnin Jurgen Roters suka samu halarta.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar raya al’dun musulunci da ke karkashin karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke kasar Jamus cewa, an gudanar da bukin bude wani babban masallaci a birnin Kolen na kasar Jamus, wanda jami’an gwamnati da suka hada magajin garin birnin Jurgen Roters suka samu halarta gami da wakilan cibiyoyin musulmi na kasar.
Gina masallacin zai taimaka matuka ma musulmi wajen gudanar da harkokinsu na bai daya, bisa la’akari da cewa an gina masallacin a baban gari wanda ke da mabiya addinin musulunci da yawa, kuma masallacin yana girma da zai iya daukar dubban mutane, daga cikin lamurran da za a rika gudanarwa a cikinsa harda sallolin yau da kullunm da kuma sallar juma’a.
Gudanar da bukin bude wani babban masallaci a birnin Kolen na kasar Jamus, wanda jami’an gwamnati da suka hada magajin garin birnin Jurgen Roters suka samu halarta, na nuni ne da cewa musulmi ba su da matsala da sauran bangarori da ma addinai.
744051




captcha