IQNA

An Baiwa Birnin Karbala Lambar Yabo Ta Addini Ta Kasar Iraki A Shekara Ta 2010

16:02 - February 09, 2011
Lambar Labari: 2078540
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin kula da gudanar da shirye-shirye na addinin Musulunci da kuma gyaran mahalli na kasar Iraki, ya bayar da lambar yabo ga Ayatollah Mahdi karbala'i babban limamin Karbala, a matsayin mutumin da ya taka gagarumar rawa ta fuskacin addini a cikin shekara a matsayin mai wakiltar birnin mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun an bayyana cewa, kwamitin kula da gudanar da shirye-shirye na addinin Musulunci da kuma gyaran mahalli na kasar Iraki, ya bayar da lambar yabo ga Ayatollah Mahdi karbala'i babban limamin Karbala, a matsayin mutumin da ya taka gagarumar rawa ta fuskacin addini a cikin shekara a matsayin mai wakiltar birnin mai alfarma a cikin shekara ta 2010.

Babban sakataren kwamitin Ali khafaji ya bayyana cewa, wakilin marja'iyya a birnin Karbala Ayatollah mahdi karbala'i mutum ne da ya cancanci wannan yabo, domin kuwa ya taka gagarumar rawa waje kusanto da fahimtar juna tsakanin al'ummomin kasar Iraki, 'yan sunna da kuma mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah.

Kwamitin kula da gudanar da shirye-shirye na addinin Musulunci da kuma gyaran mahalli na kasar Iraki, ya bayar da lambar yabo ga Ayatollah Mahdi karbala'i babban limamin Karbala, a matsayin mutumin da ya taka gagarumar rawa ta fuskacin addini a cikin shekara a matsayin mai wakiltar birnin na karbala.

744129
captcha