Kamfanin dillancin labaran Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Palasdinawa goma ne suka sami raunuka a harin ranar ashirin ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya da jiragen yaki n asama mallakar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai wa yankin zirin Gaza.Daga cikin wadanda suka jikkatan akwai wata mata guda da wani yaro lamarin da ke bayyana harin zalunci da aka kaiwa mazauna yankin zirin gazar a daidai lokacin da suke kokarin tashin asubahi.
745294