Bangaren kasa da kasa, Tashar sadarwa ta sunna da ilmomin hadisai da ke karkashin cibiyar yada sakonin musulunci ta kasar Saudiya da ke da babban ofishi a birnin Riyad ta fara aikewa da sakonni na hadisan manzo ta hanyar wayar salula zuwa ga kwastomomi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muhit an bayyana cewa, Tashar sadarwa ta sunna da ilmomin hadisai da ke karkashin cibiyar yada sakonin musulunci ta kasar Saudiya da ke da babban ofishi a birnin Riyad ta fara aikewa da sakonni na hadisan manzo ta hanyar wayar salula zuwa ga kwastomomi da ke amfani layin sadarwa na kamfanin.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar yin hakan ita ce tunatar da musulmi koyarwar hadisan ma’aiki tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka, musamman abubuwan da ya kamata mutane su rika aikawata a cikin rayuwarsu ta zamantakewa.
Tashar sadarwa ta sunna da ilmomin hadisai da ke karkashin cibiyar yada sakonin musulunci ta kasar Saudiya da ke da babban ofishi a birnin Riyad ta fara aikewa da sakonni na hadisan manzo ta hanyar wayar salula zuwa ga kwastomomin kasar.
745364