IQNA

Taro Kan Makomar Harkar Saka Hannayen Jari A Kasashen Musulmi A Bahrain

21:37 - February 12, 2011
Lambar Labari: 2079650
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani zaman na yin bita kan ayyuka da kuma harkokin saka hannayen jari a kasashen musulmi, wanda aka gudanar a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, tare da halartar masana kan harkokin kudi da tattalin arziki na kasashen musulmi da na larabawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tradearabia.com cewa, An gudanar da wani zaman na yin bita kan ayyuka da kuma harkokin saka hannayen jari a kasashen musulmi, wanda aka gudanar a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, tare da halartar masana kan harkokin kudi da tattalin arziki na kasashen musulmi da na larabawa musamman na yankin gabas ta tsakiya.
Babban daraktan cibiyar da ta hada wannan shiri Ahmad Fauzi ya gabatar da jawabi, kamar yadda jakadan kasar Malazi a Bahrain shi ma ya gabatar jawabi kan muhimman abubuwan da ya kamata a yi la’akari da su, kamar yadda babban daraktan gudanarwa na bankin Elaf shi ma ya gabatar da nasa bayanin.
An gudanar da wani zaman na yin bita kan ayyuka da kuma harkokin saka hannayen jari a kasashen musulmi, wanda aka gudanar a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, tare da halartar masana kan harkokin kudi da tattalin arziki na kasashen musulmi.
745346


captcha