Bangaren kasa da kasa, An riga an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta garin ra'asul khaima da ke cikin kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar mahardata da makaranta daga sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran wam cewa, an riga an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta garin ra'asul khaima da ke cikin kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar mahardata da makaranta daga sassa daban-daban na kasar musamman ma a birnin.
Bayanin ya ci gaba da cewa gasar na samun halartar kimanin mutane 99 daga cikin makaranta da mahardata maza, kamar yadda take samun halartar makaranta da mahardata mata daga sassa daban-daban na kasar, inda dukkanin bangarorinsu sukae karawa da juna.
Yanzu haka dai an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta garin ra'asul khaima da ke cikin kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar mahardata da makaranta daga sassa daban-daban na kasar ta hadaddiyar daular larabawa.
746252