IQNA

Jami'ar Ghana Za Ta Dauki Bakuncin Gudanar Da Taron Maktabar Imam Sadiq (AS)

15:45 - February 13, 2011
Lambar Labari: 2080274
Bangaren kasa da kasa, Jami'ar kasar Ghana da ke birnin Akra za ta daukin bakuncin shirya gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani, mai taken maktabar ilimi ta Imam Ja'afar sadiq (AS) tare da halartar manayan malamai na addinin Musulunci da kuma masana.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na karamin ofishin jakadancin Iran da Gahana cewa, jami'ar kasar Ghana da ke birnin Akra za ta daukin bakuncin shirya gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani, mai taken maktabar ilimi ta Imam Ja'afar sadiq (AS) tare da halartar manayan malamai na addinin Musulunci da kuma masana daga jami'oin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai yi dubi ne kan muhimmancin bahasi kan maktabar ilimi da Imam Sadiq (AS) ya bar wa al'ummar musulmi, wanda akasarin musulmin duniya ba su san da ita ba, inda mabiya tafrkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) ne kawai suke bin diddiginta a bincikensu.

Jami'ar kasar Ghana da ke birnin Akra za ta daukin bakuncin shirya gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani, mai taken maktabar ilimi ta Imam Ja'afar sadiq (AS) tare da halartar manayan malamai na addinin Musulunci da kuma masana na kasar.

746151



captcha