IQNA

An Sake Bude Ajujuwan Koyar Da Harshen Farisanci A Kasar Girka

Bangaren al’adu da fasaha, An sake bude wasu ajujuwan koyar da harshen farisanci a kasar Girka bayan da aka rufe su tsawon shekaru tara da suka gabata, wanda yanzu haka aka kammala dukkanin shirye-shiyen fara karatu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin yada al’adu da ke karkashin karamin ofishin jakadancin Iran an bayyana cewa, an sake bude wasu ajujuwan koyar da harshen farisanci a kasar Girka bayan da aka rufe su tsawon shekaru tara da suka gabata, wanda yanzu haka aka kammala dukkanin shirye-shiyen fara karatu ga masu sha’awar koyon harshen.
Daya daga cikin ayyukan da ofishin jakandancin kasar Iran ya gudanar a kasar ta fuskacin bunkasa lamurran da suka danganci al’adu suna da dama, amma mafi muhimmanci daga cikinsu ga kasar shi ne bude ajujuwan koyar da harshen farisanci.
Sake bude wasu ajujuwan koyar da harshen farisanci a kasar Girka bayan da aka rufe su tsawon shekaru tara da suka gabata, wanda yanzu haka aka kammala dukkanin shirye-shiyen fara karatu, hakan na da muhimmanci ga masu koyon harshen.
745924