IQNA

Baje Kolin Rubutun Musulunci A Halb

Bangaren al'adu da fasaha; kasuwar baje kolin rubutun Musulunci da na larabci da aka bawa sunan yin bita kan tarihin harafin larabci da ofishin al'adu na birnin Halb na kasar Suriya ya shirya.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kasuwar baje kolin rubutun Musulunci da na larabci da aka bawa sunan yin bita kan tarihin harafin larabci da ofishin al'adu na birnin Halb na kasar Suriya ya shirya.Wannan taro an fara gudanar da shi ne a ranar sha tara ga watan Bahman da kuma aka ci gaba da gudanar da shi har zuwa ranar ashirin da shidda ga watan Bahaman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya inda masana harkar zane da rubutu kan alluna suka hallara da nuna salon aikin kowa daga cikinsu inda masu kollo ke nasu aikin.


746945