Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a birnin Dubai babbar cibiyar kasuwanci ta kasar hadaddiyar daular larabawa daga daren jiya, tare da halartar manyan malaman addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo khaleel Times cewa, an fara gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a birnin Dubai babbar cibiyar kasuwanci ta kasar hadaddiyar daular larabawa daga daren jiya, tare da halartar manyan malaman addinin muslunci daga sassa daban-daban na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a kowace shekara kungiyoyin addini suna shirya gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) amma a wannan shekarar taron ga alama ya dauki sabon salo, sakamakon karbuwa da ya samu daga malaman addinin Musulunci na kasar, duk kuwa da babban tasirin wahabiyancin da ke kasar.
An fara gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a birnin Dubai babbar cibiyar kasuwanci ta kasar hadaddiyar daular larabawa daga daren jiya, tare da halartar manyan malaman addinin muslunci.
746865