IQNA

Gudanar Da Tarukan Addini Da Kuma Na Agaji A Kasar Faransa

14:15 - February 14, 2011
Lambar Labari: 2080806
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da taron bude wata hanya ta kafa wata tawagar aikewa da taimakon kayayyakin agaji ga al'ummar yankin Zirin Gaza da ke Palastinu, da ke fama da danniya da killacewa daga haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saphirnews cewa, an bude wata hanya ta kafa wata tawagar aikewa da taimakon kayayyakin agaji ga al'ummar yankin Zirin Gaza da ke Palastinu, da ke fama da danniya da killacewa daga haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya ta Isra'ila.

Wannan tawaga za ta hada wakilan kungiyoyi daga likitoci da kuma na lauyoyi gami da masu kare hakkin bil adama da ke fadin kasar, haka nan kuma sauran kungiyoyin mabiya addinin muslunci za su shiga cikin tawagar da kungiyoyin larabawa.

An bude wata hanya ta kafa wata tawagar aikewa da taimakon kayayyakin agaji ga al'ummar yankin Zirin Gaza da ke Palastinu, da ke fama da danniya da killacewa daga haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya.

746662





captcha