Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani zaman taro na khatmar kur'ani mai tsarki a tsibirin Burnai, tare da halartar jami'an gwamnati da kuma wakilan kungiyoyin Musulunci da cibiyoyin kur'ani na kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Brita News an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro na khatmar kur'ani mai tsarki a tsibirin Burnai, tare da halartar jami'an gwamnati da kuma wakilan kungiyoyin Musulunci da cibiyoyin kur'ani na kasar baki daya.
Rahoton ya ce kafin gudanar da wannan taro an an bayar da horo ga dukkanin matan da suka shiga cikin shirin na khatma, wanda kuma yin hakan ne ma ya sanya daga karshe aka yanke shawarar bayar da dama gare su gudanar da taron khatma, inda aka baiwa kowace daya daga cikin 'yan matan takar shedar karatu.
An gudanar da wani zaman taro na khatmar kur'ani mai tsarki a tsibirin Burnai, tare da halartar jami'an gwamnati da kuma wakilan kungiyoyin Musulunci da cibiyoyin kur'ani na kasar, wadda daya ce daga cikin kasashen musulmi masu himma wajen gudanar da ayyukan kur'ani.
747510