IQNA

Gasar Karatu Da Hardar Kur'ani mai Tsarki Ta Alhasawi A kasar Kuwait

13:38 - February 16, 2011
Lambar Labari: 2081616
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da shirye-shiryen gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta Alhasawi a kasar Kuwait, wadda cibiyar bunkasa harkokin kur'ani ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karo na biyar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ra'ay ta kasar Kuwait an bayyana cewa, an fara gudanar da shirye-shiryen gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta Alhasawi a kasar Kuwait, wadda cibiyar bunkasa harkokin kur'ani ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karo na biyar a kasar.

Wannan gasa dai ana gudanar da ita ne a bangarori daban-daban na hardar kur'ani, inda mahardata suke nuna bajinta wajen shiga cikin ayoyi da sururin kur'ani, kamar yadda makaranta da suka shara ta fuskacin tilawar kur'ani mai tsarki a kasar sukan halarci wannan gasa.

Yanzu haka dai an fara gudanar da shirye-shiryen gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta Alhasawi a kasar Kuwait, wadda cibiyar bunkasa harkokin kur'ani ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karo na biyar kamar yadda bayanin ya nuna.

748185




captcha