IQNA

Masana'antun Musulmi Na Samun Gagagarumin Ci Gaba A Kasar Malazia

13:40 - February 16, 2011
Lambar Labari: 2081617
Bangaren kasa da kasa, Masana'antun da ke tafiyar da ayyukansu bisa tsari na ciyar harkokin kudi ta Musulunci dake karakshin bankin Musulunci a kasar Malazia na samun gagagrumin ci gaba cikin sauri a dukkanin fuskoki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mysinchew an bayyana cewa, Muhammad Akram aldin babban daraktan bankin Musulunci na duniya ya bayyana cewa, masana'antun da ke tafiyar da ayyukansu bisa tsari na ciyar harkokin kudi ta Musulunci dake karakshin bankin Musulunci a kasar Malazia na samun gagagrumin ci gaba cikin sauri a dukkanin fuskoki na kasuwanci da kuma tattalin arziki.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya tana daya daga cikin manyan cibiyoyin kasar da suke taka gagarumar rawa wajen samar da hanyoyi na aikin yi, kamar yadda ayyukansu suke da gagarumin tasiri a wajen habbaka tattalin arzikin kasar.

Babbar manufar samar da wannan cibiya dai ita samar da wata dama ta musamman ga musulmi ta yadda za su iya karfafa tattalin arzikinsu na daidaiku da kuma a matsayi na gwamnatoci da kasashensu.

Masana'antun da ke tafiyar da ayyukansu bisa tsari na ciyar harkokin kudi ta Musulunci dake karakshin bankin Musulunci a kasar Malazia na samun gagagrumin ci gaba cikin sauri a kasar.

747890





captcha