Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani babban taron addini a birnin Karbala mai alfarma na kasar Iraki, da aka yi wa take daminar sako, wanda ya yi daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) da musulmi suke gudanarwa a fadin duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkauthar an bayyana cewa, za a gudanar da wani babban taron addini a birnin Karbala mai alfarma na kasar Iraki, da aka yi wa take daminar sako, wanda ya yi daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) da musulmi suke gudanarwa a fadin duniya baki daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai samu halartar manayan malaman addini daga sassa daban-daban na kasar Iraki, da suka hada da 'yan sunna da kuma mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) kuma za a gudanar da taron ne a hubbarori masu tsarki na Imam Hussain (AS) da kuma Abul Fadl (AS) da ke birnin.
Ali Saffar daya daga cikin wadanda suke gudanar shirye-shiryen taron ya bayyana cewa, bababr manufar wanna taro mai albarka dai it ace samar da hanyoyi na hada kan al'aummar musulmi ta hanayar raya muhimman ranaku masu albarka a cikin addinin muslunci.
Yanzu haka majiya ta tabbatar da cewa za a gudanar da babban taron addini ne a birnin mai alfarma na kasar Iraki, da aka yi wa take daminar sako, wanda ya yi daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a ko'ina.
748098