Bangaren kasa da kasa, an buga tare da fitar da wani bababn littafin addinin Musulunci, bayan gudanar da bincike mai zurfi dam asana a jami'ar banglor ta kasar India suka yi, kuma wallafa wannan littafi na da'iratul ma'arif a cikin mujalladai biyu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Arab news an habarta cewa, an buga tare da fitar da wani bababn littafin addinin Musulunci, bayan gudanar da bincike mai zurfi dam asana a jami'ar banglor ta kasar India suka yi, kuma wallafa wannan littafi na da'iratul ma'arif a cikin mujalladai biyu manya-manya.
Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin masanan wadanda maiya addinin Musulunci ne sun gudanar da bincike tare da yin namijin kokari na wallafa wannan babban littafi, da nufin kara wayar da kan sauran al'ummomin duniya musamman na kasashen yammacin turai da suke da mummnar fahimta kan addinin Musulunci.
An buga littafin ne a cikin harshen turancin ingishi, kuma akwai yiwuwar nan gaba a tarjama shi zuwa wasu harsuna musamman ma larabci da kuma urdu da ma wasu harsunan kamar farisanci da sauransu.
An wannan bababn littafin addinin Musulunci ne, bayan gudanar da bincike mai zurfi da masana a jami'ar banglor ta kasar India suka yi, kuma wallafa wannan littafi na da'iratul ma'arif a cikin mujalladai biyu da shafuka dubu daya da dari uku.
747969