IQNA

Gasar Karatun Kur'ani Mai Tsarki A Jahar British Colombia Da Ke Canada

14:14 - February 17, 2011
Lambar Labari: 2082359
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar musulmin kasar Canada ta shirya gudanar da wata gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a jami'ar British Colombia a cikin shekara mai kamawa, wadda za a gudanar a karo na goma.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bcmuslims cewa, kungiyar musulmin kasar Canada ta shirya gudanar da wata gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a jami'ar British Colombia a cikin shekara mai kamawa, wadda za a gudanar a karo na goma a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki za a gudanar da ita ne a mataki biyu, bangaren harda, wanda zai fara daga juzu'i na daya zuwa na biyar, hakan nan kuma daga na biyar zuwa goma a haka har zuwa karshen kur'ani.

Bayanin kungiyar musulmin kasar Canada da ta shirya gudanar da wata gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a jami'ar British Colombia a cikin shekara mai kamawa, wadda za a gudanar a karo na goma, ya ce gasar za ta fara ne watan farko.

749021





captcha