Bangaren kasa da kasa, Mabiya addinin Musulunci na kasar Ethiopia sun gudanar da taron mauludin manzon Allah (SAW) a ranar goma sha biyu ga watan rabiul awwal, wanda ya yi daidai da ranar haihuwarsa bisa ruwayoyi na mabiya tafarkin sunna.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na waltainfo an bayyana cewa, mabiya addinin Musulunci na kasar Ethiopia sun gudanar da taron mauludin manzon Allah (SAW) a ranar goma sha biyu ga watan rabiul awwal, wanda ya yi daidai da ranar haihuwarsa bisa ruwayoyi na mabiya tafarkin sunna wanda kuma akasarin musulmi suna gudanar da tarukan ne daga wadannan ranaku.
Daga cikin muhimman abubuwan da suka wakana a wajen taron har da gabatar da jawabai da kuma laccoci ga mahalarta taron, inda aka raba bayanan a matsayin makaloli da za a iya karantawa a kowane kan rayuwar manzon Allah (SAW).
Mabiya addinin Musulunci na kasar Ethiopia sun gudanar da taron mauludin manzon Allah (SAW) a ranar goma sha biyu ga watan rabiul awwal, wanda ya yi daidai da ranar haihuwarsa bisa ruwayoyi na mabiya tafarkin sunna.
748831