IQNA

An Fara Ginin Wani Babban Masallaci A Birnin Sharja Na Kasar UAE

18:21 - February 17, 2011
Lambar Labari: 2082485
Bangaren kasa da kasa, An fara ginin wani katafaren masallaci a birnin Sharjah na kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar wasu manyan jami'an daular da suka hada da sheikh Sakar Bn Muhammad Alkasimi babban daraktan hukumar kula da ayyukan addini.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar khalee jtime cewa, an fara ginin wani katafaren masallaci a birnin Sharjah na kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar wasu manyan jami'an daular da suka hada da sheikh Sakar Bn Muhammad Alkasimi babban daraktan hukumar kula da ayyukan addini ta kasar.

Wannan masallaci na daya daga cikin masallatan kasar da za a rika gudanar da salloli na kullum rana wanda zai dauki mutane da dama, yanzu haka dai an riga an dora tubalin ginin masallacin wanda ma'akatar kula da ayyukan addinin muslunci ta kasar za ta taimaka wajen aiwatar da shi.

Fara ginin wani katafaren masallaci a birnin Sharjah na kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar wasu manyan jami'an daular da suka hada da sheikh Sakar Bn Muhammad Alkasimi babban daraktan hukumar kula da ayyukan addini, na tabbatar da ci gaban da ake samu.

748816





captcha