Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na wam na kasar hadaddiyar daular larabawa cewa, za a gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka yi lakabi da gasar Alsawi ta za ta kebanci nakasassu a birnin Sharja na kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda kuma daya ne daga cikin biranan kasashen larabawa da kan dauki bakuncin gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka dai an zabi mutane 100 ne wadanda suka nuna kwazo a gasar da aka gudanar a lokutan baya, wadanda kuma awannan karon sun e za su hadu su kara da juna, inda za a fitar da wadanda za su matakai na daya da na biyu da kuma matsayi na karshe na uku.
Wannan gasa zai dai ba za ta kebanci mutanen birnin Sharja ba kawai ,za ta hada nakassasu ne daga dukkanin sassa na kasar hadaddiyar daular larabawa kamar dai yadda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar ta sanar.
Gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka yi lakabi da gasar Alsawi ta za ta kebanci nakasassu a birnin Sharja na kasar hadaddiyar daular larabawa, na nu da ci gaban da aka samu ta wannan fuska.
749762