IQNA

An Girmama Wadanda Suka Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani A Dubai

12:44 - February 19, 2011
Lambar Labari: 2083168
Bangaren kasa da kasa, An girmama makaranta duka suka halarci gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta hadaddiyar daular larabawa a cikin gidan kason birnin.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Khalij Times cewa, an girmama makaranta duka suka halarci gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta hadaddiyar daular larabawa a cikin gidan kason birnin da ke cikin kasar ta UAE.

An gudanar da taro na musamman ne domin girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar daga cikin mazauna gidan kaso, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban mahalarta taron shugaban cibiyar kula da ayyukan kur'ani da kuma harda na birnin Dubai Ibrahim Bu Malha ya bayyana jidadinsa da hakan.

Ya ce tun kafin wannan lokacin sun fara gudanar da shiri na hardar kur'ani mai tsarki wanda wasu daga cikin wadanda ake tsare da su a gidan kaso suka nuna sha'awarsu ta shiga cikin shirin kur'ani, wanda hakan ne ya bayar da damar fara gudanar da shirin tun daga farko kuma ga shi ya ci nasara.

Girmama makaranta duka suka halarci gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta hadaddiyar daular larabawa a cikin gidan kason birnin, na nuni da samun ci gaba da wannan fuska.

749803

captcha