Bangaren kasa da kasa, An bude babbar kasuwar baje littafai ta kasa da kasa a birnin Najaf mai alfarma na kasar Iraki tare da halartar cibiyoyin buga littafai da madaba'antu na kasashen musulmi, inda suke nuna littafansu a wurin.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun an bayyana cewa, an bude babbar kasuwar baje littafai ta kasa da kasa a birnin Najaf mai alfarma na kasar Iraki tare da halartar cibiyoyin buga littafai da madaba'antu na kasashen musulmi, inda suke nuna littafansu a wurin da ake gudanar da irin wannan babban taro.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje kolin littafai shi ne irinsa na hudu da ake gudanarwa a birnin, yanzu haka dai cibiyoyi da dama da suka hada manyan cibiyoyin addini na birnin Qom suna halartar wannan baje koli, kamar wasu cibiyoyin daga kasashen larabawa da na musulmi.
An bude babbar kasuwar baje littafai ta kasa da kasa a birnin Najaf mai alfarma na kasar Iraki tare da halartar cibiyoyin buga littafai da madaba'antu na kasashen musulmi, inda suke nuna littafansu a wurin gudanar da tarukan baje koli.
749790