IQNA

Majalisar Mabiya Mazhabar Iyalan Gidan Manzo A Labanan Ta Yi Suka Kan Kashe Mutane A bahrain

20:38 - February 20, 2011
Lambar Labari: 2084087
Bangaren siyasa da zamantakewa, babbar majalisar koli ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzo a kasar Labanan ta yi kakkausar suka kan kisan gilla da mahukuntan kasar Bahrain suke yi wa masu gudanar da zanga-zangar cikin ruwan sanyi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, babbar majalisar koli ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzo a kasar Labanan ta yi kakkausar suka kan kisan gilla da mahukuntan kasar Bahrain suke yi wa masu gudanar da zanga-zangar cikin ruwan sanyi a fadin kasar.
Ayatollah Abdulamir Qabalan mataimakin shufgaban majalisar mabiya mazhabar shi’a a kasar Lebanon a cikin wani bayani da ya fitar ya kira ga mahukuntan kasar Bahrain da su yi amfani da hankali wajen warware koke-koken da mutane suke yi a kasar maimakon daukar matakan yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe zanga-zangar da fararen hula suke gudanarwa.
Babbar majalisar koli ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzo a kasar Labanan ta yi kakkausar suka kan kisan gilla da mahukuntan kasar Bahrain suke yi wa masu gudanar da zanga-zangar cikin ruwan sanyi a birninManama.
750270


captcha