IQNA

An Gudanar Da Taron makon Hadin Kai A Mahangar Imam Khomeini (RA) A Zimbabwe

20:41 - February 20, 2011
Lambar Labari: 2084088
Bangaren siyasa da zamantakewa, An gudanar da wani zaman taro na makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a babban masallacin Hifield da ke cikin birnin harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a mahangar marigayi Imam Khomeini (RA) daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar bunkasa al’adu da ilimin musulunci ta kasar Iran an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro na makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a babban masallacin Hifield da ke cikin birnin harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a mahangar marigayi Imam Khomeini (RA) daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, zaman taron wanda aka gudanar a birnin Harare, ya samu halartar mutane da suka hada malamai da kuma sauran mabiya a ddinin musulunci mazauna kasar da kuma ‘yan asalin kasar,inda suka saurari bayanai da aka gabatara wajen taron.
An gudanar da wani zaman taro na makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a babban masallacin Hifield da ke cikin birnin harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a mahangar marigayi Imam Khomeini (RA) daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidi.
749792


captcha