IQNA

Za A Gudanar Da Wani Baje Kolin Littafan Musulunci A Kasar Amurka

20:40 - February 20, 2011
Lambar Labari: 2084090
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani baje kolin littafan musulunci kamar yadda aka gudanar da gasar kur’ani a garin richmond da ke cikin jahar Virginia a kasar Amurka, wanda cibiyar harkokin addinin muslunci ta jahar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a nan da makonni uku masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiya harkokin muslunci ta jahar Virginia an bayyana cewa, za a gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki a garin richmond da ke cikin jahar Virginia a kasar Amurka, wanda cibiyar harkokin addinin muslunci ta jahar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a nan da makonni uku masu zuwa, tare da halartar daliban makarntu na mabiya addinin muslunci da ke cikin jahar.
Bayanin ya ci gaba da cewa za a kasa gasar ne zuwa kashi biyu, inda za ta kunshi kanan yara da kuma masu manyan shekaru, inda dukkaninsu za su gudanar da gasar ne a bangaren da aka saka su, duk kuwa da banbancin bangarorin da za agudanar da hardar a sashen yara da kuma manya.
Bayanin ya ci gab ada cewa yanzu haka an kammala karbar sunayen masu sha’awar shiga gasar da suka yi rijista da cibiyar, inda nan ba da jimawa za a sanar da sunayen da aka dauka, wadanda su en za su kara da juna a gasar.
Za a gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki a garin richmond da ke cikin jahar Virginia a kasar Amurka, wanda cibiyar harkokin addinin muslunci ta jahar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a nan da makonni uku masu zuwa.
750109


captcha