Bangaren kasa da kasa, A yau ne za a gudanar da taron maulidin manzon Allah (SAW) a birnin London na kasar Birtaniya, wanda babbar cibiyar kula da ayyukan addinin musulunci ta birnin za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ic-el an bayyana cewa, a yau ne za a gudanar da taron maulidin manzon Allah (SAW) a birnin London na kasar Birtaniya, wanda babbar cibiyar kula da ayyukan addinin musulunci ta birnin za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a babban ofishinta.
Taron zai samu halartar mabiya addinin musulunci da ke zaune a birnin da kuma wakilan kungiyoyin bincike da suka hada da na mabiya sunna da kuma mabiya amzhabar yalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa.
A yau ne za a gudanar da taron maulidin manzon Allah (SAW) a birnin London na kasar Birtaniya, wanda babbar cibiyar kula da ayyukan addinin musulunci ta birnin za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
750851