Bangaren kasa da kasa, Daya daga cikin masu adawa da gwamnatin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya da ke zaune a birnin London na kasar Birtaniya ya sheda cewa, Imam Musa Sadr da Gaddafi ya kama shi tun sama da shekaru talatin da suka gabata yana tsare a wani gidan kaso da ke yankin Sabha.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da Abdulmajid Mansur daya daga cikin masu adawa da gwamnatin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya da ke zaune a birnin London na kasar Birtaniya ya sheda cewa, Imam Musa Sadr da Gaddafi ya kama shi tun sama da shekaru talatin da suka gabata yana tsare a wani gidan kaso da ke yankin Sabha da ke kudancin kasar.
Ya ce mahukuntan kasar Libya sun sha yin karya dangane da makomar Imam Musa Sadr bayan da suka kame shi a lokacin da yake gudanar da wata ziyara a kasar, bayan da Gaddafi ya gayyace shi, inda suke cewa ya bar kasar, amma dukkanin dalilai sun tabbata da cewa yana nan tsare a kasar.
Daya daga cikin masu adawa da gwamnatin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya da ke zaune a birnin London na kasar Birtaniya ya sheda cewa, Imam Musa Sadr da Gaddafi ya kama shi tun sama da shekaru talatin da suka gabata yana tsare a wani gidan kaso da ke kudanci Libya.
751910