Bangaren kasa da kasa, An kafa wata makarantar koyon kur'ani mai tsarki a birnin Burama da ke yankin Audal na kasar Somalia, wanda cibiyar bunkasa harkokin kur'ani ta yankin ta dauki nauyin budewa a karon farko.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Somaliland press an bayyana cewa, an kafa wata makarantar koyon kur'ani mai tsarki a birnin Burama da ke yankin Audal na kasar Somalia, wanda cibiyar bunkasa harkokin kur'ani ta yankin ta dauki nauyin budewa a karon farko a yankin.
Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin bude wannan makaranta an gudanar da gagarumin buki da ya samu halaratr manyan malaman addinin musulunci daga yankin, da suka hada limamai da kuma daliban addini, gami da 'yan jarida, haka nan kuma an gabatar da jawabai dangane da muhimmancin koyar da kanan yara karatu da harder kur'ani mai tsarki.
An kafa wata makarantar koyon kur'ani mai tsarki a birnin Burama da ke yankin Audal na kasar Somalia, wanda cibiyar bunkasa harkokin kur'ani ta yankin ta dauki nauyin budewa a karon farko.
751846