Bangaren kasa da kasa, shugaban kwamitin malaman addinin musulunci na duniya Yusuf Kardawi ya fitar da wata fatawa da a cikinta yake halasta jinin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu'ammar Gaddafi, kan kasha mutane kasarsa da yake yi ba kakkutawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya samu daga shafin sadarwa na yanar gizo na nasij an bayyana cewa, shugaban kwamitin malaman addinin musulunci na duniya Yusuf Kardawi ya fitar da wata fatawa da a cikinta yake halasta jinin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu'ammar Gaddafi, kan kasha mutane kasarsa da yake yi ba kakkutawa tun bayan da suka fara bore kimanin mako guda ya gabata.
A wata zantawa ta kai tsaye da ta hada Kardawi da gidan talabijin din Aljazeera ya bayyana cewa, bias la'akari da matakin dabbanci da rashin imani da Gaddafi ya dauka kan mutanen kasarsa musulmi da suke neman sauyi, inda yake kasha sub a tare da wani dalili ba, hakan ya halasta jininsa.
Kardawi ya ce ayar kur'ani da ke halasta jinin wadanda suke yin barna a bayan kasa ta hau kan Gaddafi kuma shi n eke misalta wadanda ake nufi a cikin wannan aya, a kan haka ya zama halas a zubar da jinisa bayan day a zubar da jinin daruruwan musulmi.
Shugaban kwamitin malaman addinin musulunci na duniya Yusuf Kardawi ya fitar da wata fatawa da a cikinta yake halasta jinin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu'ammar Gaddafi, kan kasha mutane kasarsa da yake yi.
751953