IQNA

Kwamitin Malaman Musulunci Na Duniya Ya Yi Allawadai Da Mahukuntan Libya

19:25 - February 23, 2011
Lambar Labari: 2085544
Bangaren kasa da kasa, babban kwamitin malaman addinin musulunci na duniya ya yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da mahukuntan kasar Libya, kan yadda suke yin amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar neman kauye sauyi a cikin harkokin mulkin kama karya na shugaban kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nasij an bayyana cewa, babban kwamitin malaman addinin musulunci na duniya ya yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da mahukuntan kasar Libya, kan yadda suke yin amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar neman kauye sauyi a cikin harkokin mulkin kama karya na shugaban kasar ta Libya Mu'ammar Gaddafi.

A daya bangare kuma shugaban kwamitin malaman addinin musuluncin na duniya Yusuf Kardawi ya fitar da wata fatawa da a cikinta yake halasta jinin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu'ammar Gaddafi, kan kasha mutane kasarsa da yake yi.

A wata zantawa ta kai tsaye da ta hada Kardawi da gidan talabijin din Aljazeera ya bayyana cewa, bias la'akari da matakin dabbanci da rashin imani da Gaddafi ya dauka kan mutanen kasarsa musulmi da suke neman sauyi, inda yake kasha sub a tare da wani dalili ba, hakan ya halasta jininsa.

Kardawi ya ce ayar kur'ani da ke halasta jinin wadanda suke yin barna a bayan kasa ta hau kan Gaddafi kuma shi n eke misalta wadanda ake nufi a cikin wannan aya, a kan haka ya zama halas a zubar da jinisa bayan day a zubar da jinin daruruwan musulmi.

751816
captcha