Bangaren kasa da kasa;cimma nasarar tabbatar da hadin kai a duniyar musulmi yana bukatar wani shiri na musamman tsararre day a ginu karkashin ilimi da bincike kuma malaman duniyar musulmi dole su lura amincewa da kokarin daidaiku kamar jagoran juyin juya halin musulunci na Iran da hakan zai taimaka wajan cimma burin da aka sa gaba.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; cimma nasarar tabbatar da hadin kai a duniyar musulmi yana bukatar wani shiri na musamman tsararre day a ginu karkashin ilimi da bincike kuma malaman duniyar musulmi dole su lura amincewa da kokarin daidaiku kamar jagoran juyin juya halin musulunci na Iran da hakan zai taimaka wajan cimma burin da aka sa gaba.Ahmad Alzain shugaban hadinkan kungiyar malaman musulunci a kasar Labanon a cikin wani jawabi day a gabatar a lokacin taron hadin kan musulmi karo na ashirin da hudu da aka gudanar a ranar talatin ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ya bayyana hakan.
752128