IQNA

Bayyana Goyan Bayan Ga Tashin Da Al'ummar Libiya Da Baharain Suka Yi

14:04 - February 24, 2011
Lambar Labari: 2085781
Bangaren siyaa da zaman takewa: dubban mutane ne a yan kasar Turkiya a ranar uku da gabata Isfand na sheakara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya suka gudanar da zanga-zangar lumana a dandalin Taksim da ke birnin Istambul inda suka nuna goyan bayansu ga Intifadar al'ummar kasashen Libiya da Bahrain.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne daga kasar ta Turkiya ya watsa rahoton cewa;
dubban mutane ne a yan kasar Turkiya a ranar uku da gabata Isfand na sheakara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya suka gudanar da zanga-zangar lumana a dandalin Taksim da ke birnin Istambul inda suka nuna goyan bayansu ga Intifadar al'ummar kasashen Libiya da Bahrain.Irin wannan zanga –zangar lumana da jerin gwanon nuna goyan baya an gudanar da shi a kasashe da daman a duniya inda al'ummomi ke nuna yadda suke tare da al'ummar kasashen na Bahrain da na Libiya masu yunkurin zaman da yanci da kubuta daga yan mulkin kama karya a kasashensu kamar yadda al'ummomin suka gudanar da zanga-zangar goyan baya ga al'ummomin Tunusiya da Masar.

752222

captcha