Bangaren kasa da kasa, Musulmin kasar Rasha suna samun sakonni na lokutan ibada daga 'yan uwansu mabiya addinin muslunci na kasar, ta yadda za su iya samunmasaniya kan lokutan salla da sauran lokutan ibada na musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkausar an bayyana cewa, Musulmin kasar Rasha suna samun sakonni na lokutan ibada daga 'yan uwansu mabiya addinin muslunci na kasar, ta yadda za su iya samunmasaniya kan lokutan salla da sauran lokutan ibada na musulmi da suke cikin sassa daban-daban na kasar ta Rasha.
Bayanin ya ci gaba da cewa wadannan sakonni ana aikewa da su ne ta hanyoyi daban-daban da suka hada wayar salula da kuma yanar gizo, kuma sakonni gajeru ne da za su tunatar da mutum lokutan gudanar da ibadarsa.
Da dama daga cikin mabiya addinin muslunci a kasar rasha sun nuna matukar gamsuwarsu da wannan hanya ta aikewa da sakonni ga junansu, inda sukan amfana matuka ta wannan hanya tare da yin salla bisa lokaci.
Musulmin kasar Rasha suna samun sakonni na lokutan ibada daga 'yan uwansu mabiya addinin muslunci na kasar, ta yadda za su iya samunmasaniya kan lokutan salla da sauran lokutan ibada na musulmi.
753759