IQNA

Malaman Shi'ar Kasar Indiya na Goyan Bayan Tashin Al'ummar Bahrain

10:32 - February 27, 2011
Lambar Labari: 2086966
Bangaren siyasa da zamantakewa: majalisar malaman shi'a a kasar Indiya a ranar alhamis din da ta gabata biyar ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a wani zama na musamman da suka gabatar a garin Lakhunu na wannan kasar sun bayyana a fili karara cewa suna goyan bayan gwagwarmya da tsayin daka na fuskantar zalunci da al'ummar kasar Bahrain ke yi.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; majalisar malaman shi'a a kasar Indiya a ranar alhamis din da ta gabata biyar ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a wani zama na musamman da suka gabatar a garin Lakhunu na wannan kasar sun bayyana a fili karara cewa suna goyan bayan gwagwarmya da tsayin daka na fuskantar zalunci da al'ummar kasar Bahrain ke yi.Said Shabahat Husein Radawi wakilin majalisar malaman shi'a a kasar indiya ya bayyana cewa; a wani taron gaggauwa ne da majalisarsu ta yi a dakin taro na Imamiya da ke birnin Lakhunu da zummar goyan bayan al'ummar Bahrain musamman yan shi'a da ake zalumta a kasar ta Bahrain suka bayyana goyan bayansu da boren da suke yi a kasar ta Bahrain.

753310
captcha