Bangaren kasa da kasa, Babban malamin jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar Ahmad Tayyib ya bayyana cewa tsarin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya ba shi da halasci, kuma bijirewar da sojoji suke yi masa bai saba wa shari'a ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shfin sadarwa na yanar gizo na Muhit an bayyana cewa, babban malamin jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar Ahmad Tayyib ya bayyana cewa tsarin shugaban mulkin kama karya na kasar Libya ba shi da halasci, kuma bijirewar da sojoji suke yi masa bai saba wa shari'a ba kuma yin hakan halas ne.
Y ace abin da Mu'ammar gaddafi ya yin a kisan kiyashi kan al'ummar kasarsa, ya kara bayyana hakikaninsa a idon duniya, kuma ya tabbatar da cewa shi da gwamnatinsa sun ci zarafin mutanen kasa ta hanyar dabbaci da matsanancin zalunci da ba za a taba yafe masa ba.
Ahmad Tayyib ya kara da cewa jami'ar Azhar tana kallon hakan a matsayin wani wajibi na addini, kan ta bayyana wa al'ummar kasar Libya rashin halascin Gaddafi sakamakon mayar da gwamnatinsa ta mashaya jinin bayin Allah da ya yi.
Ya kira yi dukkanin kasashe da gwamnatocin musulmi da na larabawa da su yi wa Allah su yi wa ma'aiki su taka wa Gaddafi burki kan kisan gillan da yake yi wa al'ummar kasar Libya bisa zalunci.
754406