Bangaren al'adu da fasaha: daga yau ne tara ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya musulmin kasar Keniya a dalilin zagayowar irin wannan rana ta haifuwar fiyayyan halitta Muhammad Dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa za a fara gudanar da taron shekara –shekara a daidai wannan lokaci tsakanin musulmin kasar.