Bangaren kasa da kasa, Malaman mabiya mazhabar shi'a a kasar Saudiyya sun fitar da wani bayani na bai daya dake nuna cikakken goyon bayansu ga mutanen kasar Bahrain da suke gudanar da bore, domin neman kawo sauye-sauyen siyasa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rasid an bayyana cewa, Malaman mabiya mazhabar shi'a a kasar Saudiyya sun fitar da wani bayani na bai daya dake nuna cikakken goyon bayansu ga mutanen kasar Bahrain da suke gudanar da bore, domin neman kawo sauye-sauyen siyasa a kasar ta Bahrain.
Bayanin malaman ya jinjinawa mutanen kasar Bahrain, domin kuwa sun kwashi tsawon lokaci suna fuskantar zalunci da danniya daga mahukuntan kasar 'yan mulkin mulukiya, wadanda turawan mulkin Birtaniya suka dora tun sama da shekaru biyu da suka gabata.
Aakasarin mutanen kasar Bhrain dai mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah ne, wadanda aka haramtawa dukkanin hakkokinsu na 'yan kasa, bugu da kari kan hakan ana matsa lamba kansu domin su mika wuya ga zalunci da danniyar da ake yi musu.
Malaman mabiya mazhabar shi'a a kasar Saudiyya sun fitar da wani bayani na bai daya dake nuna cikakken goyon bayansu ga mutanen kasar Bahrain da suke gudanar da bore, domin neman kawo sauye-sauyen siyasa.
755157