Bangaren al'adu da fasaha:an tarjama da watsa littafin da ya kumshi dokokin tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran a cikin yaren Garji kuma ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a ketare ne ya dauki nauyin wannan aiki.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an tarjama da watsa littafin da ya kumshi dokokin tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran a cikin yaren Garji kuma ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a ketare ne ya dauki nauyin wannan aiki.Wannan tarjamar zai bawa masu Magana da wannan harshe damar samun damar sanin irin dokokin da kundin tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran ya kumsa da kuma irin banbancinsa da sauran tsarin mulkin na sauran kasashen dab a su da tsari irin na musulunci da al'adun musulmi.
755200