Bangaren ilimi da nazari:taron karawa juna sani kan kyawawan dabi'un a aikace da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Nigeria ya dauki dawainiyar gudanarwa a birnin Lagos tare da hadin guiwar kungiyar musulunci ta Alsaburun kuma a ranar takwas ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka gudanar da taron.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; taron karawa juna sani kan kyawawan dabi'un a aikace da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Nigeria ya dauki dawainiyar gudanarwa a birnin Lagos tare da hadin guiwar kungiyar musulunci ta Alsaburun kuma a ranar takwas ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka gudanar da taron.Abdulkarim Aulawala Paramula malamin jami'a a jahar Lagos kuma sakataren wannan kungiya a cikin jawabin da ya gabatar ya bayyana cewa ko shakka babu tsari daya tilo da ke aiki da shikashikan musulunci aduniya shi ne tsarin mulkin na musulunci a Iran.
755187