Bangaren siyasa da zamantakewa;sheikh Abu Ja'afar Muhammad Jabate yana daya daga cikin fitattun malaman juma'a a kasar Mali dangane da nuni da ci gaban musulunci a kasarsa ta Mali ya bayyana cewa; al'adun al'ummar kasar ta Mali da ke yammacin nahiyar Afrika ya samo tushe ne daga al'adun musulunci da larabci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; sheikh Abu Ja'afar Muhammad Jabate yana daya daga cikin fitattun malaman juma'a a kasar Mali dangane da nuni da ci gaban musulunci a kasarsa ta Mali ya bayyana cewa; al'adun al'ummar kasar ta Mali da ke yammacin nahiyar Afrika ya samo tushe ne daga al'adun musulunci da larabci.Kuma wannan ya samo asali ne daga yadda al'ummar kasar ta Mali suka karbi addinin musulunci a tsawon lokaci da kuma yadda suke cuduwa da larabawa daga zuwa yankin don kasuwanci ko wani dalili na daban da kuma yadda yan malin musulmi ke ta fiya aikin hajji a duk shekara.
755853